✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta yaba wa El-Rufai kan zaben Birnin Gwari da Zangon Kataf

PDP ta yabi El-Rufai kan zaben da ’yan takararta suka lashe a kananan hukumomin.

Babbar jam’iyyar adawa a Jihar Kaduna, PDP, ta jinjina wa gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, bisa yadda ya bari aka yi zaben gaskiya da adalci a zaben shugabannin kananan hukumomin Birnin Gwari da Zagon Kataf, wadanda jam’iyyar ta lashe.

Sakataren PDP na Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono, shi ne ya yi yabon a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

“Babu shakka wannan abu da aka yi, zai kawo dawamamen zaman lafiya da cigaba a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya, musamman a bangaren harkokin siyasa,’’ inji Wusono.

Ya ce ita kanta Shugabar Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna, Saratu Audu Dikko, ta yi adalci a zabubbukan da aka gudanar.

A cewarsa, sun yi mamakin ganin yadda El-Rufai ya bari aka yi zaben gaskiya da adalci a kananan hukumomin biyu, ya kuma ba da umarnin cewa duk wanda ya ci a ba shi.

Bayan an yi zaben PDP ta ci, kuma ya yarda aka ba da sanarwa cewa PDP ce ta ci wadannan zabubbuka.