Babbar jam’iyyar adawa a Jihar Kaduna, PDP, ta jinjina wa gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, bisa yadda ya bari aka yi zaben gaskiya da adalci a zaben shugabannin kananan hukumomin Birnin Gwari da Zagon Kataf, wadanda jam’iyyar ta lashe.
Sakataren PDP na Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono, shi ne ya yi yabon a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
- So muke kotu ta ba da umarnin cire Kudu maso Gabas daga Najeriya —’Yan Arewa
- Dole Shugaban Kasa ya zama Musulmi Bayarabea 2023 —MURIC
“Babu shakka wannan abu da aka yi, zai kawo dawamamen zaman lafiya da cigaba a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya, musamman a bangaren harkokin siyasa,’’ inji Wusono.
Ya ce ita kanta Shugabar Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna, Saratu Audu Dikko, ta yi adalci a zabubbukan da aka gudanar.
A cewarsa, sun yi mamakin ganin yadda El-Rufai ya bari aka yi zaben gaskiya da adalci a kananan hukumomin biyu, ya kuma ba da umarnin cewa duk wanda ya ci a ba shi.
Bayan an yi zaben PDP ta ci, kuma ya yarda aka ba da sanarwa cewa PDP ce ta ci wadannan zabubbuka.