✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta sake ɗage babban taronta

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabanninta na ƙasa karo na 99 da ta shirya gudanarwa ranar 28 ga watan…

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabanninta na ƙasa karo na 99 da ta shirya gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamban nan.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu ya fitar ranar Alhamis.

Anyanwu ya ce an ɗage taron shugabannin jam’iyyar karo na 99 saboda mambobinsu su samu damar halartar jana’izar mai ɗakin Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno da za a yi.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyya, ke samun saɓani da rikice-rikice tsakanin ’ya’yanta.

Tun bayan da wata kotu ta sanar da cire shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Iyorchia Ayu a 2023, jam’iyyar ta sanar da naɗa Ilya Damagum a matsayin shugabanta na riƙo.

To sai dai shi ma Damagun ya riƙa fuskantar suka daga wasu ’ya’yan jam’iyyar — waɗanda suka riƙa kiraye-kirayen ya sauya daga muƙamin.

A taronsu karo na 98 da suka gudanar cikin watan Afrilu, shugabannin jam’iyyar sun amince da kafa kwamitocin sasanci da na ladabtarwa da shirya tarukan jam’iyyar tun daga matakin mazaɓu zuwa jihohi.

A bayan nan PDP ta ɗage taronta wanda tun da farko aka shirya gudanar da shi a watan Agusta gabanin mayar da shi zuwa watan Satumba.

Daga nan PDP ta sake mayar da taron ranar 24 ga watan Oktoba, sannan kuma ta sake ɗage shi zuwa 28 ga Nuwamba.

Da yake yi wa wasu matasan Arewa ta Tsakiya jawabi a Abuja, tsohon mai magana da yawun PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya ce yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar biyayya ita kaɗai hanyar da za ta kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka addabi jam’iyyar da kuma Najeriya baki ɗaya.

Dangane da shugabancin jam’iyyar, Ologbondiyan ya ce yankin Arewa ta Tsakiya zai ci gaba da faɗi tashin ganin an mallaka masa haƙƙinsa.