✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta nemi gafarar ‘Yan Najeriya bisa kura-kuranta na baya

A ranar Litinin da ta gabata ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi afuwar ’yan Najeriya game da dukan kura-kuran da ta yi a…

A ranar Litinin da ta gabata ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi afuwar ’yan Najeriya game da dukan kura-kuran da ta yi a tsawon shekara 16 da ta shafe tana mulkin kasar nan.

Shugaban Jam’iyyar, Uche Secondus ne ya nemi afuwan a yayin wani taron tattauna lamuran da suka shafi kasa da jam’iyyar ta shirya a Abuja, mai taken: “Contemporary Gobernance in Nigeria.” Mista Secondus ya ce, a madadin ilahirin ’ya’yan jam’iyyar tasu ta PDP, suna neman afuwar dukan ’yan Najeriya dangane da laifuffukan da suka hada da karfa-karfa wurin tsayar da ’yan takara da rashin hukunta masu laifuffuka da sauransu. 

Haka ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa, a karkashin kulawarsa, babu yadda za a yi ya yarda a yi karfa-karfa wurin tsayar da ’yan takara. “A matsayina na Shugaban Jam’iyyar, na amince cewa Jam’iyyar PDP ta tafka kura-kurai a baya; kuma mu mutane ne da kan iya aikata laifuffuka, amsa laifinmu shi ne alamun cewa za mu gyara. Mun san cewa mun tafka kurai-kurai masu dimbin yawa, saboda haka muna da darussan da babu wata jam’iyya da ke da irinsu. 

“Kamar yadda ’yan Najeriya suka gaji da mu, har suka sauya mu a zaben shekarar 2015, ina amfani da wannan damar wurin bayyana tubarmu da neman afuwa kan kura-kuran da muka aikata a baya,” inji Secondus. Ya ce, ba za su sake maimaita irin baram-baramar da suka tafka a baya ba.

“Mun nemi jama’ar Najeriya su yafe mana ne domin mun tabbatar da cewa mun dauki darussa sosai daga kura-kuran baya, don haka yanzu mun sanya alkiblarmu ta wata hanyar ta daban domin samar da ingantacciyar jam’iyya mai tsari,” inji shi.

 Shugaban na PDP ya sha alwashin cewa tunda sun gano kura-kuransu, ba za su yarda su sake maimatawa ba; don haka ya bukaci al’umma’ar kasar nan su kwantar da hankalinsu su kuma sake aminta da jam’iyyar domin a yanzu sun sauya alkibla ta yadda ya dace. 

Sai dai a martanin da Ministan Labari Alhaji Lai Mohammed ya mayar, ya ce sai wadanda suka yi mulki a karkashin PDP sun amayo dukiyar da suka sace ne tubar tasu za ta karbu a wurin ’yan Najeriya. Minista Lai wanda ya mayar da martani a madadin gwamnati ya ce, ba ta furuci kawai ya kamata PDP ta tuba ba, sai ta hada da aiki wajen dawo da dukiyar sata.