Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta nemi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kori Ministansa na Ma’aikatar Sadarwa, Isa Pantami kan kalaman da ya yi a baya na nuna goyon baya ga kungiyoyin Al Qaeda da Taliban.
Cikin sanarwar da PDP ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta na kasa, Kola Ologbondiyan, ta bayyana damuwarta a kan barin Pantami ya ci gaba da kasancewa Ministan Sadarwa a kasar.
- An kai wa ofishin ’yan sanda hari a Anambra
- Ganduje ya kaddamar da sabbin baburan kama masu laifi a Kano
A baya bayan nan ne aka zargi Ministan da tsattsauran ra’ayi bisa wasu kalamai da ya yi can da dadewa wanda ya nuna goyon bayansa a kan wasu kungiyoyin ta’adda.
Sai dai Ministan a ranar Asabar yayin gabatar da tafsirin AlKur’ani na watan Azumi a Masallacin Al Noor da ke birnin Abuja, ya yi watsi da kalaman da ya yi a shekarun baya wadanda suka haifar da cece-kuce a ’yan kwanakin nan.
“Lokacin da na yi wadancan kalamai a shekarun baya da a yanzu suka janyo cece-kuce, inda karancin shekaru da kuma yadda na fahimci addini addini a wancan lokaci, kuma a yanzu na sauka daga wannan matsayi kuma na sauya akida bayan na kara fahimtar addini,” inji Pantami.
Sai dai PDP duk da wannan karin haske da bayanin watsi da akidarsa ta baya da Ministan ya yi, ta ce ba zai yiwu a ci gaba da amincewa da shi ba a matsayin mai rike da duk wasu muhimman bayanai na kasar nan ba.
Ministan wanda ke fuskantar kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa saboda wadancan kalamai, ya danganta su da ayyukan abokan gaba wadanda ke adawa da shirin da yake aiwatarwa a cikin gwamnati musamman na hada lambar zama dan kasa da layukan wayoyin sadarwa.
Pantami ya ce babu tababa cikin wannan matsayi na shi na cewar wannan zargi da ake masa nada nasaba da rajistar da gwamnati ta bukaci kowa ya yi, ganin cewar tun daga shekarar 2011 a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan aka dauko shirin amma bai samu nasara ba saboda yadda wasu ke adawa da shi.
Ministan ya yi karin haske kan shirin rajistar wanda a cewarsa ya shafi duk mazauna Najeriya da suka wadanda suka fito daga wasu kasashen domin tattara bayanan kowane dan kasa da baki kamar yadda doka ta yi tanadi.
Ya ce idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wa gwamnati wajen rage aikata laifuffuka saboda yadda za a rika amfani da bayanan wajen gano masu laifi cikin hanzari.
Kazalika, Ministan ya ce adawa da yarfen da ake masa ba za su hana shi ci gaba da abin alherin da ya kudirta ba, sannan kuma ba za su janye masa hankali daga kyakkyawan aikin da ya sanya a gaba ba.