Jam’iyyar PDP ta lashe zaben duka kujerun shugabannin kananan hukumomi 16 da aka gudanar a Jihar Taraba.
Philip Duwe, Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Taraba (SIEC) ne ya bayar da bayanin haka yau Lahadi, lokacin da yake bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin a hedikwatar hukumar da ke Jalingo.
- Super Eagles ta kara tuntube a wasan neman gurbin Gasar Kofin Duniya
- Kotun Daukaka Kara ta kori Gwamnan Jihar Filato
Duwe ya kuma ce sakamakon zaben kujerun kansiloli 165, an bayyana shi a hedikwatar hukumar da ke kowace karamar hukumar.
“Jam’iyyu 6 ne suka yi takara a zaben, amma PDP ce ta lashe duk kujerun kamar yadda sakamakon ya nuna.”
“Muna godiya ga ’yan jaridu, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da suka sanya ido kan yadda zaben ya gudana,” in ji Shugaban Hukumar Zaben Taraba.
Ya kuma ce suna jiran rahoton kungiyoyin da suka sanya ido, domin sanin wajen da suka yi kuskure, inda ya dau alkawarin za su gyara gabanin zaben da za su shirya a gaba.
Bayanai sun ce a gobe Litinin ce Gwamna Agbu Kefas zai rantsar da sabbin shugabanin kananan hukumomin da safe a filin wasa na Jolly Nyame da ke birnin Jalingo.