Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Bauchi ta lashe dukkan kujerun ciyamomi da kansiloli a zaben kananan hukumomin da ya gabata ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jihar (BASIEC), Dahiru Tata shine ya bayyana hakan a ranar Lahadi lokacin da yake raba takardun shaidar lashe zaben a Bauchi.
- APC ta lashe zaben duk kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi
- Tsohon minsta ya lashe zaben gwamnan Bauchi
Ya ce, “Zaben ya gudana cikin lumana, kuma PDP ta lashe dukkan kujerun kananan hukumomi 20 na jihar da kansilolu 323.
“Wannan shine sakamakon da dukkan turawan zabe suka bayyana a matakai daban-daban, nan kuma mun taru ne domin mu raba musu takardun shaidar lashe zaben,” inji Dahiru.
A wani labarin kuma, ana nan ana dakon wasu shari’u guda hudu a Babbar Kotun Tarayya dake Bauchi da wasu jam’iyyu suka kan shigar kan cire sunansu daga zaben.
Da yake jawabi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), sabon zababben shugaban karamar hukumar Bauchi, Mahmood Baba-Ma’aji ya yabawa alu’mmar karamar hukumar tasa bisa amincewa da suka yi da shi.
“Na gamsu da yadda. zaben ya wakana.
“Za mu tabbatar mun tafi da kowa wajen kawowa karamar hukumarmu ci gaba.
“Akwai kalubale a kanmu da yawa, amma za mu yi iyakar iyawarmu wajen ganin mun ba mara da kunya,” inji shi.