✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta kwace duk kujerun sanatocin APC a Kaduna

A yanzu dai jam'iyar PDP ce ta lashe dukkan kujerun sanatoci uku da ke a Jihar Kaduna

A yanzu dai jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe daukacin kujerun Sanata uku da Jihar Kaduna ke da su.

PDP ta yi nasarar kawo kujerarta na Kaduna ta Kudu, inda Marshal Katung ya yi nasara, sannan za ta maye gurbin sanatoci biyu masu ci na APC a jihar.

Sanatocin APC da ba za su koma kan kujerunsu su ne Suleiman Abdu Kwari na Kaduna ta Arewa da kuma Sanata Uba Sani na Kaduna ta Tsakiya, wanda yanzu yake neman takarar gwamnan jihar.

Dan takarar Sanata a PDP, Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mista LA, ne ya lashe kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, inda ya kayar da Abdullahi Muhammad Sani Dattijo na APC.

A Kaduna ta Arewa kuma, Muhammad Khalil na PDP ne ya kayar da Sanata Suleiman Abdu Kwari da ke neman tazarce.

Hakazalika a zaben shugaban kasa, PDP ta lallasa APC mai mulkin jihar, inda ta ci kananan hukumomi 14 dga cikin 23 da ke jihar.