Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce jam’iyyar PDP ta dawo don ta karbi mulki a shekarar 2019 inda za ta yi jagoranci nagari.
Goodluck Jonathan ya yi furucin ne a babban taron jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, jiya.
A ranar 12 ga watan Julin da ya gabata ne kotun koli ta kawo karshen rikita-rikitar shugabancin da ta shiga tsakanin Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Ali Madu Shariff, inda kotun ta tabbatar da shugabancin Sanata Ahmed Makarfi.
Tsohon Shugaban Kasar ya bayyana cewa duk da jam’iyyar ta sha fama da rikicin shugabanci saboda faduwa zaben da ta yi a shekarar 2015 to amma har yanzu ita ce jam’iyya mafi girma a daukacin Afirka.
Jonathan ya bayyana cewa zai yi wuya ga duk wata jam’iyya har da jam’iyyar APC da take mulki ta kayar da jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa na shekarar 2019.
Ya bayyana bukatar da ke akwai na jam’iyyar ta karbi mulki saboda abin da ya kira tsananin talauci da yunwa da ke kasar.
Saboda haka sai ya bukaci shugabannin jam’iyyar da dattawanta da kuma masu ruwa da tsaki su koma jihohinsu su wayar da kan jama’arsu kan zaben 2019.