✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta ci zaben gwamna a Filato, jihar jagoran yakin zaben Tinubu

APC ce ke mulkin jihar, kuma Gwamna Simon Lalong shi ne babban daraktan yakin neman zaben Tinubu

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Barista Caleb Mutfwang na Jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Filato.

Jam’iyyar APC ce ke mulkin jihar, kuma Gwamna Simon Bako Lalong shi ne babban daraktan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC na kasa.

Ko a zaben shugaban kasa da aka gudanar, jam’iyyar LP ce ta samu kuri’u mafi yawa a jihar, duk da matsayin Gwamna Lalong a APC.

Da yake sanar da sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, baturen zaben kuma Jami’ar tarayya da ke Lafiya, Farfesa Idris Amali, ya bayyana cewa Barista Caleb Mutfwang, ne ya yi nasara da kuri’u 525,299.

Babban abokin takararsa, Farfesa Nentawe Yilwada, na Jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’u 481,370.