Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, ya bukaci a kama dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da karkatar da halasta kudaden haramun a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas.
Kwamitin ya yi kira ga Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, (NDLEA) da Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Kasa Zagon Kasa (EFCC) da su gaggauta cafke Tinubu tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.
- NIS ta damke ‘yan ci-rani 303 a Akwa Ibom
- Mutum 8 cikin kowanne 10 a China na dauke da COVID-19 – Rahoto
PDP ta yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben, Mista Daniel Bwala, ya bukaci NDLEA da ta gayyaci Tinubu domin yi masa tambayoyi kan wata badakalar Dala 460,000 da ya yi tsawon shekaru a kasar Amurka.
Bwala, wanda ya kuma yi Allah wadai da kwamitin da Tinubu ya kafa, wanda ya bayyana shi a matsayin ‘yan bindiga, ya bukaci hukumomin tsaro da su kama su sannan su gurfanar da duk wanda ke cikin kwamitin da ake kira da ‘Jagaban Army’.
Ya kara da cewa ‘yan adawa da dama na fuskantar barazana gabanin zaben da ake shirin shiga.
Wani mai magana da yawun kamfen na PDP, Phrank Shaibu, ya yi zargin cewa har yanzu Tinubu na ci gaba da gudanar da kasuwancin haramtattun kwayoyi tun daga 2015 zuwa yanzu.
Ya kara da cewa, Tinubu ya aike Dalar Amurka miliyan 4.3 zuwa wani kamfani da ke Kasar Colombiya.
A satin da ya gabata ne dai, mai magana da yawun kwamitin yakin zaben APC, Festus Keyamo, ya aike wa EFCC da ICPC takarda kan bukatar su cafke Atiku.
Keyamo ya zargi Atiku da hannu wajen gudanar da wasu harkalloli da suka yi sama da fadi da dukiyar jama’a a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasa.