Kwamitin Tsarin Karba-karba na uwar Jam’iyyar PDP ya ba wa yankin Arewa kujerar Shugaban Jam’iyya na Kasa gabanin zaben 2023.
Shugaban Kwamitin kuma Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwanyi, shi ne ya sanar da hakan ranar Alhamis bayan wani zama da suka yi a Abuja.
Mista Ugwanyi ya ce Kwamitin Gudanarwar PDP na Kasa ya amince a yi musayar mukaman jam’iyyar tsakanin yankin Kudu da Arewa.
Sai dai ya bayyana cewa aikin da aka ba wa kwamitinsa bai shafi kujerar dan takarar shugaba kasa da mataimakinsa ba.
Sanarwar mayar da shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Arewa ta biyo bayan taron da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta yi ne a daren Alhamis.
A lokacin taron tara daga cikin gwamnonin sun goyi bayan a mayar da shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Arewa, uku kuma suka zabi a mayar zuwa yankin Kudu.