Jam’iyyar PDP a jiya ta kaddamar da kwamitin sasantawa wanda ta dora masa alhakin dawo da tsofaffin ’ya’yanta cikin jam’iyyar.
Kwamitin dai Gwamna Nyeson Wike na jihar Ribas da takwaransa na jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ne ke jagorancinsa.
Jam’iyyar ta kaddamar da kwamitin shirya babban taron jam’iyyar da kuma kwamitin ladaftarwa wanda Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Cif Tom Ikimi suke jagoranta.
Jam’iyyar ta kaddamar da kwamitocin ne a taron da ta gudanar a Otel din Chida da ke Abuja.
Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na jam’iyyar, Sanata Ahmed Makarfi ya ummarci kwamitin sasantawar ya tabbatar da ya dawo da Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da wasu manyan tsofaffin ’ya’yanta cikin jam’iyyar.
Shugaba Obasanjo ya yaga katinsa na jam’iyyar PDP a wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo dabda babban zaben shekarar 2015 inda ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar sannan shi ma Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar a shekarar 2014.