Kwamitin tantance ’yan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, ya ce biyu daga cikin masu neman takarar sun yi asarar kudin fom dinsu sakamakon gaza cika sharudan da jam’iyyar ta gindaya musu.
Kwamitin dai na karkashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
- Harin bam ya hallaka mutane da dama a masallacin Afghanistan
- 2023: An saya wa Tinubu fom din takarar APC kan miliyan N100m
Akalla dai akwai mutum 17 da ke hankoron samun tikitin tsaya wa jam’iyyar takara a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Kwamitin, dau ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Juma’a a Abuja bayan kammala aikin tantance ’yan takaran.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Sanata Mark ya ce PDP ba za ta mayar wa ’yan takara biyun da suka gaza kai bantensu kudaden da suka sayi fim ba, wadanda yawansu ya kai Naira miliyan 40.
Sai dai, Sanata Mark ya ki bayyana sunayen wadanda lamarin ya shafa, inda ya ce, “Kada ma ku tambayi wadanda lamarin ya shafa.”