Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kai tsaye a Abuja ranar Juma’a.
- Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia
- An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno
Daily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin adawa a faɗin ƙasar nan na ƙara zage damtse wajen ganin sun ƙulla alaƙa da nufin kawar da Jam’iyyar APC.
Sai dai kuma, mabambantan buƙatu tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattaunawar ƙawancen da suke yi.
Da yake bayani a yayin taron manema labarai, Wike ya ce: “PDP ba ta shirya zaɓen 2027 ba, a bayyane yake, misali ina da jarrabawa kuma zan je aji don karatu, shin ina yin karatun? Ina fahimtar karatun? Ba ka buƙatar ka yaudari wani da cewa kana karatu. Kana ƙoƙarin zuwa karatun ne kawai don mutane su ga cewa ka ɗauki jakarka zuwa aji.
“Halin da PDP ke ciki ke nan, don haka ba za su iya cewa tabbas sun shirya wa zaɓen 2027 ba, gwagwarmayar neman mulki ba za ta iya taimakawa jam’iyyar ba.”