✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Pantami zai maka kafar da ta zarge shi da ta’addanci a kotu

Babu ko da makamancin sunasa a cikin mutanen da hukumar tsaro ta FBI take nema

Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya sanar cewa zai maka kafar da ta yada labarin karya cewa kasar Amurka na neman sa bisa zargin ta’addanci.

Aminiya ta gano cewa labarin karya ne ya yi ta yawo cewa Amukra ta sanya sunansa a cikin jerin mutunen da take nema bisa zargin daukar nauyin ta’addanci.

“Na gani kun janye labarin bayan binciken da kuka gudanar. Amma aikin jaridar binciken kwakwaf yana bukatar a yi binciken kwakwaf kafin a wallafa. Nan gaba manyan wadanda suka wallafa labarin za mu hadu da su a gaban kotu kan wannan cin mutunci.”

Ta kuma gano cewa babu ko da kalmar Pantami, ballantana wani mutum mai suna Isa Ali, ko Isa Ibrahim, ko makamancin haka a cikin jerin mutanen da hukumar tsaro ta FBI ta Amurka take nema bisa zargin ta’addanci a cikin kasar ko a kasashen duniya.

Kazalika, babu wata babbar kafar yada labarai mai zaman kanta da ta ruwaito labarin da ya tayar da kura.

Muna nema afuwan Minista

Kafar NewswireNGR da ta ruwaito labarin daga Daily Independent ta janye labarin da ta wallafa tare da cewa, “Muna neman afuwar masu karatu saboda labarin da muka wallafa, muna kuma neman yafiyar Ministar Sadarwan Najeriya, Sheikh Isa Pantami.

“Mun gudanar da bincike mai zaman kansa a kan labarin [namu] kuma muka gano cewa ba daga hukumar Amurkan (ta FBI) da aka ruwaito ya fito ba.”

Za mu hadu a kotu —Pantami

Amma a sakon da ya wallafa a shafinsa, Pantami ya ce kotu ce za ta raba shi da NewswireNGR.

“Nan gaba za mu hadu da manyan wadanda suka wallafa labarin a gaban kotu kan cin mutuncin da suka yi min,” inji shi.

“Janyewar ba ta isa ba”

Tuni wasu ’yan Najeriya suka fara bayyana ra’ayoyinsu a kan lamarin, inda yawancinsu ke shawartar Ministan ya maka kafar newswire a kotu.

Hadimin Shugaban Kasa, kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce, “@NewsWireNGR kun dauka cewa janye labarin da kuka yi ta isa ta gyara ta kuma dakatar da barnar da labarinku ya yi wa @DrIsPantami?”

Tsoho takwaransa na Gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) ya ce, “@DrIsaPantami, don Allah kar ka amince da janyewar. Ka samu wani Babban Lauya Najeriya (SAN) mai rai da lafiya, ya maka su a kotu. Labarin ya riga ya karade kafafen sada zumunta, kuma sun riga sun bata maka suna; ya kamata a buga misali da wasu daga cikin kafafen intanet ’yan farfaganda.”

Neman zubar da kima ne —Uwa

Janyewar na zuwa ne a daidai lokacin da kakakin Ministan, Uwa Sulaiman, ta fitar da sanarwa cewa labarin ba shi da makama.

Ta ce hankali ba zai dauka ba a ce duk da irin ayyukan da Pantami yake yi na yaki da ta’addanci, a same shi da hannu a abin da ake zargin.

“Tsare-tsaren farko da ya kawo a matsayinsa na Minista sun hada da yin rajistar layukan waya da nufin dakile ayyukan ta’addanci, wanda ya taka burki ga yadda a baya ake sayarwa da kuma yin rajistar layukan waya barkatai.

“Hade layukan waya da lambar dan kasa ta NIN da ake yi a yanzu kuma, an bullo da shi ne domin tabbatar da ganin tsarin rajistan layin wayan ya yi karko.

“Saboda haka babu yadda za a yi duk mutum mai lissafi ya je ya wallafa irin wannan labarin,” inji ta.

Uwa, ta kuma yi waiwaye ga barazanar hallaka Pantami da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi saboda tsarin rajistar da rufe layukan waya marasa rajista da Ministan ya kawo.

Ta ce, “Ko dai har an manta barazar da Shekau ya yi masa ne, bayan da Ministan ya birkita musu lissafi, suka kasa ci gaba da harkokinsu yadda suka saba?”

Ko kafin NewswireNGR ta janye labarin, Daily Independent da ta wallafa labarin da aka gano cewa shaci-fadi ne, ta ambato wani hadimin Pantami –wanda ba ta bayyana sunansa ba– yana karyata labarin a matsayin na kanzon kurege.

“Wannan yunkuri ne kawai na zubar da mutunci da cin zarafin addinin da akidar mutum. Babu wani abin da Gwamnatin Amurka take zargin sa da aikatawa,” inji hadimin Ministan cikin bacin rai.

Ita ma Uwa, ta bayyana wa Sashen Hausa na BBC cewa, “An buga labarin ne da zummar bata sunan ministan.

“Wasu mutane ne da suka rasa yadda za su bullo wa Pantami domin su muzanta shi – shi ne suka fake da kirkirar labarin.”

Ra’ayin Pantami ka ta’addanci

Tun kafin nada shi matsayin Minista, Pantami ya kasance shahararren mai wa’azin Musulunci ne, kuma mai farin jini.

Ya kuma dade yana caccakar ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram a yayin karatuttukansa.

A shekarun baya, ya taba yin wata zazzafar mukabala da shugaban kungiyar Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf, wanda jami’an tsaro suka kasha, inda a mukabalar Pantami ya hana shi sakat da tambayoyi da kuma ruwan hujjjoji.

Bayan zamansa Minista, Pantami ya bullo da tsare-tsare da dama ta zummar dakile kafafen gudanarwa da kuma taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Daga cikinsu akwai tsarin yi wa layukan waya rajista da kuma rufe layukan waya marasa cikakkiyar rajista.

Ya kuma bullo da tsarin hade lambar NIN da layukan waya wanda a halin yanzu a ke ci gaba da yi.

A shekarar 2020, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya da su hada kai da Ministan, domin dakile ayyukan ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya.