Majalisar Wakilai ta gayyaci Ministan Fasahar Sadarwa Isa Ali Pantami da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan rancen Dala miliyan 500 na aiki jirgin kasa da sauransu a fadin Najeriya.
Majalisar ta kuma gayyaci Ministar Kudi Zainab Ahmed Darekta Janar na Ofishin Kula da Basuka (DMO) Patience Oniha su zo tare da su domin bayani a kan rancen daga bankin shige da fice na kasar China.
Shugaban Kwamitin Sulhu da Tsare-tsare na Majalisar, Ossai Nicholas a ranar Talata ya bukaci ministocin su hallara ranar 17 ga watan Agusta.
Ossai Nicholas ya bukaci dukkansu da a kawo dukkan takardun yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da kamfanin CCECC na kasar China kan aikin jirgin kasa na Abuja-Kaduna, Lagos-Ibadan, Ibadan-Kaduna da kuma Kaduna-Kano.