Akin Osuntokun ya zama sabon Darakta-Janar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jami’yyar LP.
Ya zama sabon jagoran yakin neman zaben jam’iyyar ne bayan Babbar Kotun Tarayya ta kama Doyin Okupe, mai rike da kujerar a baya da laifin karkatar da kudaden makamai.
- Kudin Makamai: Kotu ta daure Doyin Okupe A Gidan yari
- Doyin Okupe ya yi murabus daga kwamitin yakin neman zaben Peter Obi
Idan ba a manta ba, Doyin Okupe, tsohon Hadimin tsohon shugaban kasa kan Hulda da Jama’a, ya yi murabus ne bayan kotun da ke Abuja ta kama shi da laifin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
Ya sanar da saukarsa daga mukaminsa na Darakta-Janar na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na LP ne ta wata wasika da ya aike wa dan takarar jam’iyyar, Peter Obi.
A ranar Litinin ta makon jiya kotu ta yanke wa Okupe hukuncin dauri a gidan yari kan lafin karkatar da kudaden makamai a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ta kuma ci shi tarar Naira miliyan 13, tare da ba shi zabin biyan Naira dubu 500 a maimakon kowane hukuncin da ta yanke mishi na zama a gidan yari.
Sai dai ta ce idan ya gaza biyan tarar kafin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, za a tisa keyarsa zuwa gidan yari.
A 2019, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da Doyin Okupe a gaban kotu kan tuhume-tuhume 59 kan halasta kudaden haram da karkatar da Naira miliyan 240 daga hannun Kanar Sambo Dasuki, tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro.
Alkalin kotun ta ce ta yanke hukuncin ne bayan sauraron koken neman sassauci da wasu manyan ’yan Najeriya da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife da kuma Shugaban Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), Idi Farouk da matar Okupe, molara da kuma dansa.
A cewarta Okupe ya yi jayayyar karbar miliyoyin kudaden da ake zargin sa da karkatarwa.