✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbanjo ya kai ziyarar jaje ga iyayen Hanifa a Kano

Osinbanjo ya kai ziyarar tare da jajanta wa iyayen Hanifa.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci iyayen Hanifa yarinya mai shekara biyar da ake zargin malamin makarantarsu ya kashe ta, don yi musu ta’aziyya.

Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma bayyana damuwarsa da rashin jin dadin yadda lamarin ya faru.

Ya ce “Duba da irin jajircewa da jami’an tsaro suka yi, ina da tabbacin cewar shari’a za ta yi wa wannan yarinya da ba ta san komai ba adalci.”

Yayin ziyarar ta’aziyyar dai, Osinbajo ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu jami’an gwamnatin jihar, a ranar Talata wajen kai ziyarar jajen.

Hanifa Abubakar mai shekara biyar a duniya ta gamu da ajalinta ne ta hannun malamin makarantarsu, Abdulmalik Tanko, wanda ake zargi da sace ta, ya boye ta, sannan daga bisani ya hallaka ta.

Aminiya ta rawaito yadda jami’an tsaro a Jihar suka cafke Abdulmalik, mamallakin makarantar ‘Noble Kids’ da ke Kano kan zargin yadda ya kashe ta tare da birne gawarta bayan karbar kudin fansa a hannun iyayenta.

Ya sace Hanifa a watan Disambar bara, sannan ya bukaci kudi miliyan shida daga hannun iyayenta.

A kokarin karbar kudin fansar yarinyar ne jami’an tsaro suka yi nasarar cafke shi da wasu da ake zargi da hannu a kitsa laifin.

Tanko mai shekara 34, Hashim Isyaku mai shekara 37 da Fatima Jibrin mai shekara 26, dukkaninsu mazauna unguwar Tudun Murtala a Karamar Hukumar Nassarawa a Kano, ana zarginsu da laifin hada baki, garkuwa da kuma kisa wanda hakan ya saba da sassa na 97 da 274 da kuma 277, 221 na Kundin Manyan Laifuffuka.