A ranar Talata Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai kama hanyar zuwa kasar Ghana kamar yadda fadar shugaban Najeriya ta bayyana.
Mataimakin shugaban kasar zai halarci taron Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), dangane da rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar Mali.
A cewar mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasa Mista Laolu Akande, taron da za a gudanar a birnin Accra, zai mayar da hankali wajen kawo sasanci a kan rikicin siyasar kasar Mali da ya ki ci ya ki cinyewa.
Haka kuma Farfesa Osinbajo zai gana da wakilan al’ummar Najeriya mazauna kasar Ghana domin tattaunawa a kan matsalolin da suke fuskanta.
Karamin ministan harkokin waje na Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, na daga cikin tawagar da za ta yi rakiyar mataimakin shugaban kasar zuwa makociyar kasar.