Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yana nan a Fadar Aso Rock yana aiki tukuru don ceto tattalin arzikin Najeriya.
Babban mataimaki na musamman a kan harkar yada labarai ga Mista Osinbajo, Lalolu Akande, ya bayyana haka yana fatali da kalaman da suka bi gari a kafofin sadarwa na zamani cewa babu kowa a fadar ta shugaban kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Mista Akande yana kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da yin watsi da masu kirkirar labaran bogi game da inda shugaban kasa da mataimakinsa suke.
“Dimbin al’ummarmu masu matukar muhimmanci na ganin Shugaban Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa a-kai-a-kai a talabijin, suna jin su a-kai-a-kai a rediyo, suna kuma karanta labarai game da su a jaridu sannan suna bibiyar ayyukansu a-kai-a-kai a kafofin sadarwa na zamani”, inji Mista Akande.
Muhawara dai ta barke ne a shafukan sada zumunta a karkashin wani maudu’i da ke cewa daga shugaban kasar har matakinsa sun kaurace wa fadar ta Aso Rock Villa, wanda aka yi amanna masu fafutukar Biafra ne suka yada shi.
Da ma dai a kwanan baya an fara tsegumi game da cewa tun bayan da annobar coronavirus ta barke ba a ji duriyar Mista Osinbajo ba.
Sai dai a cewar kakakin mataimakin shugaban kasar, ko a kwanakin nan ya wallafa sakwanni da dama game da ayyukan da Mista Osinbajo ke gudanarwa a shafukansa na sada zumunta.
“Misali, ranar Alhamis Mataimakin Shugaban Kasar ya halarci wata ganawa kai-tsaye ta bidiyo tare da gwamnan Kaduna, da Ministocin Wutar Lantarki da Kudi, da Gwamnan Babban bankin Najeriya (CBN) da sauran jami’an gwamnati a kan yadda za a bunkasa samar da wutar lantarki a kasar nan.
“Aiki na ci gaba, kuma tabbas Najeriya za ta yi nasara; za mu gudu tare mu tsira tare”, inji Mista Akande.