✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oscar Pistorious ya barke da kuka a kotu

Shahararren mai yi wa kasar Afirka ta Kudu gudun nakasassu  Oscar Pistorious da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa Reeba Steenkamp a shekarar bara, ya…

Shahararren mai yi wa kasar Afirka ta Kudu gudun nakasassu  Oscar Pistorious da ake tuhuma da laifin kashe budurwarsa Reeba Steenkamp a shekarar bara, ya barke da kuka a kotu a ranar Litinin da ta wuce a lokacin da aka fara sauraron shari’ar da ake masa ta laifin kashe budurwar tasa.
A lokacin da yake bayanin yadda al’amarin ya faru a gaban kotu ne sai aka ga ya sunkuya kuma ya barke da kuka yana rokon iyalan marigayiya Reeba da su yafe masa laifin kisan da ya yi wa ’yarsu a bara, kuma ya yi haka ne a bisa kuskure.
Ya ce tun ranar da ya kashe budurwar tasa a bisa kuskure a shekarar bara ya shiga mawuyacin hali don ko barcin kirki ba ya iyi a yi, da zarar ya runtse ido babu abin da yake gani sai fatalwar Reeba da hakan ta sa yake zama kamar zararre.
Wannan dai shi ne karo na farko da Oscar ya fara bayyana a kotu tun bayan da al’amarin ya faru.  An fara shari’ar ne a Kotun daukaka kara da ke Pretoria a kasar Afirka ta Kudu.
A shekarar bara ce dai Oscar Pistorious ya kashe budurwarsa Reeba Steenkamp ta hanyar harbinta da bindiga a bayan gidansa a lokacin da ta kai masa ziyarar ba-zata bayan ya dauka barawo ne yake kokarin shigar masa gida.  Al’amarin ya tayar wa iyalan Reeba hankali inda suka maka shi kotu kuma suke neman a kotu ta bi musu kadi.  Ya zuwa yanzu Alkalin kotun ya daga cigaba da sauraron karar zuwa nan gaba  bayan da Lauyoyin Oscar da na iyalan marigayiyar suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotu.