Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya lashe aman da ya yi a kan kisan sojoji 12 a Bonta dake kauyen Konshisha dake jihar inda a baya ya yi ikirarin sojoji biyu ne kawai aka kasha ba 12 ba.
Gwamnan dai ya nemi gafarar iyalan sojojin saboda kalaman nasa na baya, inda ya ce ya dauki matsayin ne sakamakon bayanan da aka ba shi a wancan lokacin.
- Pantami zai maka kafar da ta zarge shi da ta’addanci a kotu
- Mutanen gari sun kone ’yan bindiga 3 kurmus a Katsina
Ya ce, “Idan na fadi wani abu da ya bata ran iyalan mamatan, to ina neman gafararsu.
“A baya na ce sojoji biyu ne kawai aka kashe sakamakon bayanan da nake da su a lokacin,” inji shi.
Gwamna Ortom ya kuma nemi afuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.
Ya nemi gafarar ne yayin jana’izar sojojin a wata Makabartar Sojoji dake yankin Wurukum a Makurdi, babban birnin jihar.
An dai yi jana’izar su ne a gaban Gwamnan, Kwamandan Rundunar Tsaro ta Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini, Kwamandan Bataliya ta 72, sauran manyan jami’an sojoji da kuma iyalan mamatan.
Ortom ya kuma ce, “Muna Allah-wadai da wadanda suka kashe wadannan sojojin a kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya. Hari a kan jami’an tsaro hari ne a kan kowa kuma abin takaici ne,” inji shi.
Daga nan sai ya roki iyalan sojojin da su yi masa afuwa la’akari da irin bacin ran da hakan zai iya haddasa musu.