Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya gayyaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin kaddamar da wasu sabbin gine-gine a Gidan Gyaran Hali na Makurdi da ke jiharsa.
Gwamna Ortom ya bayyana hakan ne a wani taro da al’ummar Ugondo, yankin da gidan gyaran halin yake.
- Majalisar Dokokin Peru ta tsige Shugaban Kasar
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Takaita Cire Kudade Zai Sahfi Zaben 2023
Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Ortom ya sha sukar gwamnatin shugaba Buhari ta jam’iyyar APC, musamman ma dangane da hare-haren makiyaya a sassan Jihar Benuwai, wadanda suka yi sanadin rasa rayuka da lalata dukiyoyi masu tarin yawa.
Gayyatar Ortom ga Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ke tsaka da takun saka da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta PDP, Atiku Abubakar, kan zaman Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Ortom, na daga cikin gwamoni biyar na PDP da ake kira ‘G-5’ wadanda suka sanya yin murabus Ayu ya yi a matsayin sharadinsu na mara wa Atiku baya a zaben 2023.
An fara aikin gyara gidajen yarin ne bayan wasu hare-hare da aka fasa wasu gidajen yari a sassan kasar nan, ciki har da na Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ortom ya gargadi al’umma game da yin katsalandan a filin da aka bayar ga ma’aikata da duk wata hukumar tarayya da ke bayar da gudunmawar cigaban al’ummar Benuwai da kuma tsaron lafiyarsu.