Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta amince mambobinta su rage yawan man da suke hakowa kullum, a karon farko a cikin shekara guda.
Kungiyar ta nemi yin hakan ne a kokarinta na daga farashin danyen man da ya fadi warwas a bisa fargabar karayar tattalin arzikin kasashe.
- Abin kunya ne a ce har yanzu Najeriya na shigo da man fetur
- Kotun Kolin Kenya ta tabbatar da nasarar Ruto a zaben Shugaban Kasa
Sai dai wannan yunkuri ka iya tunzura Amurka saboda matsin lambar da take ta yi wa kungiyar na ta kara yawan man da ta ke haka, domin farashin makamashi ya yi kasa, wanda hakan ya hifar da tsadar kayayyaki.
Farashi man a kasuwar duniya ya yi tashin gwaron zabo, sakamakon mamaye Ukraine da Rasha ta yi, a inda ya kai Dalar Amurka 140 kan kowacce ganga.
A taron kungiyar da aka yi na karshe, an amince da karin yawan man zuwa ganga 100,000 a kowacce rana a watan Satumba bayan ziyarar shugaban Amurka Biden a kasar Saudiyya.
Ministan makamasshi na Saudiyya, Abdulaziz Bin Salman, a watan da ya gabata ya bude kofar amincewa da ragin hako danyen man, wanda ya sami amincewar yawancin kasashen ’yan kungiyar.