✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Omicron bai kai COVID-19 tsanani ba, inji WHO

WHO ta ce Omicron bai kai sauran samfuran saurin yaduwa ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sabon bincike na nuni da samfurin cutar COVID-19 na Omicron bai kai sauran nau’u’kan tsanani ba, duk da yake ya fi su saurin yaduwa.

Binciken dai ya nuna cewa samfurin na shafar hanyar numfashi ta sama, wanda yake haifar da bayyanar cutar cikin sauri, ba kamar sauran samfuran na baya ba.

“Muna ganin sabbin bincike daban-daban da ke nuni da Omicron na shafar sassan saman jiki, ba kamar sauran ba da ke haifar da matsanancin ciwon sanyi,” inji Abdi Mahamud, ma’aikacin WHO a tattaunawarsa da manema labarai a birnin Geneva.

Ya ce hakan dai na nuni da cewa Omicron za ta kewaye kusan ko ina a makonni kadan saboda yadda take da saurin yaduwa tare da haifar da barazana ga kasashen da ke da mafiya yawan yan kasarsu da ba su yi allurar rigakafi ba.

Bayanan nasa kan yiwuwar raguwar tsananin cutar ya yi daidai da bincike da dama, ciki har da wanda aka gudanar kwanan nan a Afirka ta Kudu.

Da aka tambaye shi ko kwayar Omicron na bukatar tata allurar rigakafin, Mahamud ya ce yayi wuri a yanke hukunci a kan haka, amma ya ce hukuncin na bukatar hadin kan kasashen duniya, ba wai a bar ’yan kasuwa su yanke hukuncin su kadai ba.

A wani sabon bincike, wanda ba a kammala tantance shi ba, an gano cewa Omicron na da saurin kama hanyoyin numfashi fiye da samfurin Delta da Corona ta ainihi, ko da yake bat a illata hanyoyin da gaggawa.