Rahotannin da ke fitowa sun nuna kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya kamu da rashin lafiya jim kadan bayan wasan da kungiyar Super Eagles ta yi da ta Kamaru a ranar Lahadin da ta wuce a Beljiyam. A wasan, Najeriya ce ta yi kaca-kaca da Kamaru da ci 3-0 a wasan sada zumunta da kasashen biyu suka shirya wa junansu.
Jim kadan bayan an tashi wasan ne sai kocin ya nemi izini daga shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick don ya ziyarci wani asibiti a Beljiyam don a duba lafiyarsa.
Sai dai rahoton da kafar watsa labaran wasanni ta Sportinglife.com ta kalato game da wannan batu bai bayyana takamaiman irin ciwon da kocin yake fama da shi ba. Hakan ta sa kocin bai zai halarci wasan da Najeriya za ta yi da kasar Burkina Faso na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka da zai gudana a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu ba.
Oliseh ya kamu da rashin lafiya
Rahotannin da ke fitowa sun nuna kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya kamu da rashin lafiya jim kadan bayan wasan da…
