✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Okonjo-Iweala ta kai matakin karshe a neman shugabancin WTO

Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta kai matakin karshe a fafutukar da take yi na darewa kujerar Babbar Darakta a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya…

Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta kai matakin karshe a fafutukar da take yi na darewa kujerar Babbar Darakta a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Zuwa ranar Laraba dai Ngozin da dan takarar da ya fito daga kasar Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee ne kadai suka rage a cikin ‘yan takarar bayan an yi tankade da rairaya.

Rage yawan masu takarar dai daga biyar zuwa biyu na nufin idan hakan ta tabbata, cibiyar kasuwancin dake birnin Geneva mai kimanin shekaru 25 zata kasance karkashin shugabancin mace a karo na farko.

Ita dai Ngozi kwararriya ce a harkar tattalin arziki da ci gaba kuma yanzu haka ita ce shugabar Kwamitin Rigakafi na kasa da kasa wato GAVI.

Ta sha alwashin in har ta dare kan kujerar, WTO za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin matalautan kasashe sun sami rigakafi da kuma kwayoyin yaki da cutar COVID-19.

Zuwa karshen watan Nuwamba mai zuwa dai kungiyar za ta zabi wanda zai maye gurbin shugabancinta bayan tsohon shugabanta Roberto Azevedo ya sauka daga mukaminsa shekara daya kafin karewar wa’adinsa.

Duk wanda ya sami nasarar zama sabon shugaban dai zai fuskanci babban kalubalen daidaita al’amura musamman tsakanin kasashen China da Amurka kan batun annobar COVID-19 da kuma kawo sauye-sauye.

%d bloggers like this: