Tsohuwar Ministar Kudin Najeriya, Misis Ngozi Okonjo-Iweala ta zama mace, kuma ’yar Afirka ta farko da aka nada a matsayin Babbar Darakta a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
Misis Ngozi dai za ta maye gurbin tsohon shugabar hukumar dan asalin kasar Brazil, Roberto Azevedo wanda ya ajiye shugabancin hukumar tun kafin karewar wa’adinsa a watan Agustan 2020.
Idan za a iya tunawa, tsohuwar Ministar Kudin ta Najeriya ta kasance mutum daya tilo dake neman kujerar bayan abokiyar hamayyarta ’yar kasar Koriya ta janye daga takarar a makon da ya gabata.
Da take sanar da nadin a ranar Litinin a shafinta na Twitter, WTO ta ce, “Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya ce za ta kasance sabuwar Babbar Daraktar WTO.
“Misis Ngozi ta kafa tarihin kasancewa mace, kuma ’yar Afirka ta farko da za ta shugabanci wannan hukumar. Wa’adinta zai fara ne ranar daya ga watan Maris mai zuwa.
“WTO ta yanke shawarar nadata a wannan mukami ne a karshen taron Majalisar Kolinta na musamman, bayan yin zaben da ya hada da ’yan takara guda takwas dag kasashen duniya daban-daban.”