Ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ya kama da gobara a tsakar dare kafin wayewar garin Juma’a.
Kakakin ’yan sandan Jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya ce gobarar ta tashi ne a ofishin INEC da ke Obollo-Afor, a Karamar Hukumar Udenu ta Jihar ba.
- Yadda fasto ‘ya babbake’ miloniya yayin yi masa addu’a
- Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
- Tsawa ta kashe giwaye 18 a Indiya
“Bayan samun kiran neman dauki a babban ofishin ’yan sanda na Udenu, ada misalin karfe 9.40 na dare ranar 13/05/2021, cewa gobara ta tashi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor.
“Jami’anmu da ke ofishin sun yi gaggawan isa wurin tare da sanar da hukumar kashe gobara halin da ake ciki domin a kashe wutar.
“Bayanan somin-tabi sun nuna matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar wadda ’yan kwana-kwana da ’yan sanda da mutanen gari suka yi nasarar kashewa kafin ta bazu zuwa sauran gine-ginen da ke harabar ofishin.
“Kwamishin ’Yan Sanda, Mohammed Aliyu, ya kuma sa a zurfafa bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa gobarar da kuma irin barnar da ta yi.”
Baya-bayan nan dai ana yawan kai hare-hare a kan gine-ginen gwamnati a yankin Kudu-maso-gabashin Najeriya.