Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya rushe Majalisar Zartarwarsa a ranar Juma’a yayin da yake shirin miƙa mulki ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar.
Sabon gwamnan jihar, Monday Okpebholo, zai karɓi mulki a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba.
- HOTUNA: Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi
- Fim ɗin ‘Ƙanwata ce’ yana koyar da yadda ake kare haƙƙin ƙanne mata ne – Yaron l Malam
Obaseki, wanda ya hau mulki a ranar 12 ga watan Nuwamban 2016, zai kammala wa’adinsa tare da miƙa mulki ga Okpebholo, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
Okpebholo na jam’iyyar APC, ya kayar da Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP.
Ya rushe majalisar ne bayan wani taron ban kwana a gidan gwamnatin Jihar Edo da ke Birnin Benin.
Obaseki, ya gode wa tawagarsa bisa taimakonsa wajen cimma burinsa a Jihar Edo.
Ya kuma gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayansu, addu’o’i, da haɗin kan da suka ba shi a lokacin gudanar da mulkin jihar.
A wajen taron, kwamishinonin da ke shirin barin ofis da shugabannin hukumomi daban-daban sun miƙa lambar yabo da kyaututtuka ga Obaseki yayin da yake shirin barin ofis.