✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ya musanta alaƙarsa da jam’iyyar PDP

Tsohon Shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya musanta alaƙarsa da jam’iyyar PDP batun da aka yi ta yayatawa a ƙarshen makon jiya. Cif Obasanjo ya…

Tsohon Shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya musanta alaƙarsa da jam’iyyar PDP batun da aka yi ta yayatawa a ƙarshen makon jiya. Cif Obasanjo ya musanta haka ne a taron manema labarai da ya kira a gidansa da ke Abeokuta a ranar Asabar ɗin da ta gabata
A wata takarda da aka bai wa manema labarai cikinsu har da wakilin Aminiya, da  mataimakin Cif Obasanjo na  yaɗa labarai ya rattaba wa hannu, ta nuna cewa labari a hoton da wata kafar yaɗa labarai ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, wanda yake nuni da cewa,  tsohon shugaban ƙasar ya halarci taron jam’iyyar PDP, wanda ya  gudana a Cibiyar Shehu Musa ‘Yar’aduwa a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa, mutanen da suka shirya wannan labari sun yi haka ne don su tozartashi, su ci mutuncinsa, su kuma muzguna masa. Ya ce  tuni ya bayyana wa duniya cewa, ‘ya janye hannunsa daga siyasa, kuma bakin alƙalami ya riga ya bushe.’
 “Na bar jami’iyyar a lokacin da take raye, sannan  kanta a haɗe, me kuma zai sanya in koma cikinta a lokacin da ta karkasu  gida-gida, take magagin mutuwa,” inji Obasanjo.
Ya ce a daidai lokacin da ake taron na jam’iyyar PDP ana kuma taron masu ruwa da tsaki a kan al’amuran noma a cibiyar ta Shehu Musa ‘Yar’aduwa. Kuma ya halarci taron na manoman ne a lokacin da ƙungiyar masu ruwa da tsaki suka gayyace shi a taron da suka shirya  mai taken ‘ Kawar da yunwa a Najeriya.”  Ya isa cibiyar kimanin ƙarfe 10 na safe, kuma kai tsaye ya zarce zauren taron, wanda ‘yan mintunan da suka rage kafin a fara taron ne, wasu mutane suka shigo zauren  taron suka kawo masa gaisuwa, waɗanda ya gane cewa, ‘yan siyasa a cikin barkwanci ne, inda ya ce da su masu haura shinge, bayan kammala taron  ne ya fita kai tsaye, tare da tawagarsa  suka doshi Legas, inda a nan ne ya fara jin jita-jitar bayan da aka yi ta kiransa a waya ana neman ƙarin haske game da al’amarin.
Hoton da aka yi ta yayatawa an ɗauke shi ne a lokacin da tsohon shugaban ƙasar yake ƙoƙarin fita daga cibiyar bayan  kammala taron da ya halarta, ya ce kamata ya yi jaridar da ta wallafa labarin ta san da cewa akwai zauren tarurruka, waɗanda ake gudanar da tarurruka da yawa a lokaci guda. Don haka yin bincike don ladabtar da duk masu hannu a aikin ya zama dole. Shi zai sa ya zama izna a nan gaba.