Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya kafa harsashin ginin gadar sama ta Naira biliyan 3.4 a garin Sakkwato.
Obasanjo ya ce gadar samar za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin ta fuskoki da dama idan aka yi la’akari da muhimmancin bangaren sufuri.
- Mahaifiyar Sarkin Kano ta rasu
- ’Yan bindiga sun kona gidan Gwamnan Imo, sun kashe jami’an tsaro
- Harin ’Yan bindiga: Saudiyya ta ba da tallafin abincin $1.2m a Zamfara
A cewarsa, titin saman zai inganta rayuwa da walwalar al’ummar Jihar Sakkwato, sannan ya yaba wa Gwamnan Jihar, Aminu Waziri Tambuwal wanda ya ba da aikin.
Da yake jawabi, Gwamna Tambuwal ya ce gina gadar samar tsohuwar bukata ce, saboda yanayin wurin da za a gina ta, kuma za a kammala aikin ne a cikin wata 24.
Ya ce gwamnatinsa ta kashe sama da Naira biliyan 10 a kan ayyukan hanyoyi a kwaryar birnin Sakkwato.