Allah Ya yi wa shugaban ma’aikata a fadar shugaban Najeriya Mallam Abba Kyari rasuwa bayan ya sha fama da jinyar cutar Coronavirus.
Abba Kyari ya rasu yana yi wa kasa hidima – Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga shugaba Muhammadu Buhari kan rasuwar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da iyalan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari, wanda ya rasu sanadiyyar cutar coronavirus.
A wasikar ta’aziyyar da Obasanjo, ya aikewa Shugaba Buhari ya bayyana cewa, “Wannan rasuwar ta Abba Kyari babban rashi ne ga Shugaban kasar, da iyalansa tare da abokan arziki amma a dauke ta a matsayin rashin wanda ya mutu yana yi wa kasarsa hidima”.
Ina yi wa Abba Kyari fatan Aljannah- Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da iyalan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari.
Ya yi addu’ar Allah Ya sa Aljannah ta zama makomarsa tare da bai wa iyalansa da ’yan uwansa hakurin wannan rashin.
Abba Kyari ya kasance mai biyayya ga Buhari —Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar kuma Wazirin Adamawa, shi ma ya mika sakon ta’aziyyarsa shugaba Muhammadu Buhari, game da rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari, ya kwatanta marigayin a matsayin mai biyayya ga shugabansa.
Atiku, ya sanar da hakan ne ranar Asabar inda ya ce, “Na samu sakon rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ina yin ta’aziyyar wannan rashin tare da bada hakurin rashin da aka samu.”
“Kowa ne halitta sai ya dandana mutuwa bayan rayuwar duniya.”
Wazirin Adamawa, ya tunatar da ’yan Najeriya cewa annobar coronavirus ba ta banbance mai mukamin siyasa ko wani mai mulki.
Ya kara da cewa, rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, zai bai wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa wajen yakar wannan annoba mai kisan a’lumma.
“Ina rokon Allah Ya sa aljannah ta zama makomar Abba Kyari.” In ji Atiku.