✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo bai halarci taron majalisar ƙasa da Tinubu ya kira ba

Wasu daga cikin tsofaffin shugabannin Najeriya sun halarci taron da ya gudana a Abuja.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, bai halarci zaman Majalisar Zartaswa da Shugaba Bola Tinubu, ya kira a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da Goodluck Ebele Jonathan.

Sauran tsoffin shugabannin ƙasar sun haɗa da; Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar.

Ana gudanar da taron majalisar dokokin ƙasar ne domin bai wa shugaban ƙasa shawara kan manufofin siyasa da sauran batutuwan da shugaban ƙasa mai ci zai iya sanyawa a gaba.

Mambobin majalisar sun haɗa da shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, tsofaffin shugabannin ƙasa da shugaban majalisar dattawa, sakataren gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi, shugaban majalisar wakilai da kuma babban lauyan tarayya.

Taron da aka yi, wanda shi ne na farko da gwamnatin mai ci ta haɗa, na zuwa ne kwanaki bayan da ‘yan Najeriya suka fantsama kan tituna domin nuna adawa da halin ƙunci da tsadar rayuwa da ake fama.