✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obama na shan caccaka a Indiya kan kare hakkin Musulmi

Indiya ka iya “fara balbalcewa” idan ba ta kare hakkin marasa rinjaye ba.

Shugabannin jam’iyya mai mulki a Indiya suna ci gaba da caccakar tsohon Shugaban Amurka Barack Obama game da sukarsu kan take hakkin Musulmi a kasar.

Mista Obama ya faɗa a wata hira a makon jiya cewa Indiya ka iya “fara balbalcewa” idan ba ta kare hakkin marasa rinjaye ba.

Yana amsa tambaya ce game da yadda Shugaban Amurka Mista Joe Biden ya kamata ya yi mu’amala da kasashe masu bin dimokuradiyya amma masu tsaurin ra’ayi.

Firayi Ministan Indiya Mista Narendra Modi na ziyarar aiki a Amurka a daidai lokacin.

Kuma yayin ziyarar tasa, an yi masa maraba a Fadar White House cikin shagali, da liyafar abincin dare da kuma suka sa hannu kan wasu yarjejeniyoyi.

Haka Modi ya yi wa taron hadin-gwiwar majalisun Amurka jawabi.

Kafofin labarai a Indiya sun yada hirar da Obama ya yi da wakiliyar CNN Christian Amanpour, wadda aka saki kafin ya gudanar da jawabi a majalisar.

Ta tambayi Obama: “Yaya ya kamata Shugaban Kasa ya yi mu’amala da shugabanni wajen ambaton sunansu ko hulda da su?”

Mista Obama ya ce “Abu ne mai sarkakiya,” kafin ya bayyana irin halin da ya shiga wajen hulda da kawayen Amurka da “ba sa bin salon dimokuradiyya,” amma kuma dole kasar ta ci gaba da kawance da su saboda wasu dalilai.

Ya ce “zai yi kyau” Shugaban Amurka, idan zai yiwu, ya kalubalanci “lamuran da ba su dace ba” a bayyane ko a boye.

Ya kara da cewa “Idan Shugaban Kasa ya hadu da Firayi Minista Modi, ya kamata ya kawo masa batun kare hakkin Musulmi a kasar Indiya, wadda mafi yawan al’ummarta mabiya addinin Hindu ne.”

“Idan da a ce zan tattauna da Modi a yanzu, wanda mun san juna sosai, daya daga cikin abubuwan da zan fada masa shi ne idan ba ka kare hakkin marasa rinjaye a Indiya ba, to akwai yiwuwar cewa nan gaba kasar za ta fara darewa,” in ji shi.

Mista Obama ya dasa da Modi a lokacin mulkinsa.

Ministar Kudi ta Indiya, Nirmala Sitharaman, wadda ita ma ’yar Jam’iyyar BJP ce mai mulki, ta shaida wa manema labarai cewa ta “kadu” da kalaman tsohon Shugaban Amurka Barack Obama.

Ta ce: “A daidai lokacin da Mista Modi ke bayani kan lamuran Indiya a Amurka — wani tsohon Shugaban Kasar kuma yana surutu kan Musulmin Indiya.”

Sitharaman ta kara da cewa Amurka a lokacin Obama ta jefa bama-bamai a kasashen Musulmi, kamar Siriya da Yemen.

Shi kuwa Ministan Tsaron Indiya, Rajnath Singh ya mayar da martani da cewa Indiya ba ta taba tsangwamar wasu mutune saboda addininsu ba.

Ya ce “Masu ikirarin kare hakkin tsiraru su tsaya su yi tunani kan kasashen Musulmi nawa ne suka kai wa hari.”

Gwamnatin Amurka da kuma Obama ba su ce komai ba kan jerin martanin na manyan ’yan siyasar kasar ta Indiya.