✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NYSC ta magantu kan tura masu yi wa kasa hidima yaki a Nijar

Jami’an tsaro za su kama wanda ya soma yada wannan farfaganda.

Hukumar Yi wa Kasa Hidima a Najeriya (NYSC), ta ce babu wani shiri da take yi na tura matasa masu hidimar kasa zuwa Jamhuriyar Nijar don yakar sojojin da suka yi juyin mulki. 

Kakakin NYSC, Mista Eddy Megwa, ya ce sun musanta batun ne sakamakon wani bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta.

“Babu kamshin gaskiya a labarin da wani mai shirya barkwanci ya kirkira,” in ji shi.

“Ya kamata masu yi wa kasa hidima da iyaye su yi watsi da batun, wanda aka shirya shi da zimmar tayar da zaune tsaye.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro za su kama wanda ya kirkiri bidiyon.

A ranar Juma’a ne Shugaba Bola Tinubu ya nemi goyon bayan Majalisar Dattawa don tura sojoji karkashin Kungiyar ECOWAS zuwa Nijar don su tilasta wa sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum komawa kan tsarin mulki.

Sai dai majalisar ba ta goyi bayan kudirin ba, tana mai ba da shawarar a ci gaba da yunkurin tattaunawa ta hanyar diflomasiyya.

NAN