Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta a kan Falasɗinawa da ke cikin halin kunci a Gaza ranar Idin karamar Sallah.
An kai wannan hari ne ’yan sa’o’i bayan Shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana yaƙar Falasɗinawan a matsayin kuskure.
Biden ya kuma buƙaci a tsagaita wuta har na tsawon makonni shida zuwa takwas domin a samu damar shiga da abinci da magani yankin da Isra’ila ta ɗai-ɗaita.
Wani ma’aikacin jinya a Falasɗinu, Rawan Abd ya ce wannan ita ce Sallar idi mafi rashin daɗi a tarihinsu.
“Wannan ita ce sallar idi da ta fi kowace rashin daɗi a tarihin rayuwarmu. Muna zuwa Masallacin Kudus kowace shekara domin ibada da taya juna murna, amma bana sai dai mu yi wa juna jaje da ta’aziyya.
“Duk wanda aka dubi fuskarsa za ga bacin rai da bakin ciki.”
Da ya ke martani ga kalaman Shugaban Amurkan, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, “duk duniya babu wanda ya isa ya hana su yaƙar Hamas.
Ya kuma jaddada aniyarsu ta kama mayaƙan Hamas su mayar da su fursunonin yaƙi.
Netanyahu ya kafe akan cewa “babu wanda zai hana sojojin Isra’ila shiga birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.”
Rafah gari ne da ke cike da Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu a Zirin Gaza suka koma can a matsayin ’yan gudun hijira.
Ana iya tuna cewa, Shugaban kasar Amurka Joe Biden yayin wata hira da gidan talabijin ya ce “ina da cewa fahimtar abin da Isra’ila ke yi a matsayin kuskure ne.
“Ban yarda da irin wannan tsarin ba.”
Ya buƙaci Netanyahu ya sa a tsagaita buɗe wuta, a ba da damar tsawon makonni shida zuwa takwas masu zuwa, domin a samu a shiga da abinci da magunguna kasar.
Wannan yaƙin dai ya barke ne a ranar 7 ga watan Oktoba 2023, wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane 1,170, galibi fararen hula, kamar yadda wasu alkaluman da Isra’ila ta fitar suka nuna.
Isra’ila ta kakaba wa mutanen Gaza takunkumi da ya hana su samun abinci da ruwa da man fetur da magunguna da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa .
Kungiyoyin agaji sun zargi Isra’ila da amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi a Gaza, inda ƙwararru a Majalisar Dinkin Duniya suka ce rabin al’ummar kasar na fuskantar matsalar karancin abinci.