Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) na shirin sake bude sansanonin bayar da horo da zarar an kara sassauta dokar kulle a Najeriya.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci Shugaban Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), Dokta Chike Ikweazu, a Abuja.
A wata sanarwa da ya fitar, Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Hukumar, Adenike Adeyemi, ya ce NYSC ta yanke shawarar dakatar da bayar da horo ne ga rukunin matasa na farko, zango na daya a shekarar 2020, mako guda bayan fara ba su horon don kauce wa yaduwar coronavirus.
Shugaban hukumar ya ce saboda yiwuwar dage dokar gaba daya, tuni suka tsara hanyoyin da za su bi wajen sake bude sansanonin kuma sun mika tsarin ga Kwamitin Kar-ta Kwana na Yaki da Cutar ta hannun hukumar ta NCDC domin amincewa.
- An dage horar da masu yin NYSC rukunin C na Kaduna
- NYSC ta kama masu yi wa kasa hidima 10 da takardun bogi
Janar Ibrahim ya kuma ce nan ba da jimawa ba zango na daya, rukunin farko na matasan da aka dakatar da ba su horon za su dawo sansanoninsu don kammala karbar horon da zarar kwamitin kar-ta-kwanan ya bayar da izinin yin hakan.
Bugu da kari, ya shaida gudunmawar da matasan masu yi wa kasa hidima suka bayar wajen yaki da cutar a Najeriya.
Ya ce matasan sun shirya tarukan wayar da kan jama’a a wurare da dama, sannun suka samar tare da rarraba kyallen rufe fuska, sabulu, sinadarin wankle hannu, injinan tsaftace muhalli da sauran abubuwa.
Da yake nasa jawabin, shugaban hukumar NCDC, Chike Ikweazu, ya yaba wa hukumar NYSC bisa gudunmawar da matasan suke bayarwa ta fuskar yaki da COVID-19 a Najeriya, musamman wajen samar da injinan wanke hannu da kuma na feshin magungunan kwayoyin cutar.
Ya ce hukumar tasa za ta yi duba na tsanaki a kan bukatar NYSC na sake bude sansanonin kuma za ta mika su ga duk masu ruwa da tsakin da suka dace.