✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nwoye ya lashe zaben fidda gwanin APC na Jihar Anambara

Dan Majalisar Dokoki ta Tarayya, Mista Tony Okechukwu Nwoye, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Anambara na jam’iyyar APC. Nwoye dan kimanin…

Dan Majalisar Dokoki ta Tarayya, Mista Tony Okechukwu Nwoye, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Anambara na jam’iyyar APC.
Nwoye dan kimanin shekaru 42 a duniya wanda har ila yau likita ne ya samu kuri’u dubu biyu da 146 ind hakan ya sanya ya kayar da abokin hamaiyarsa, Sanata Andy Uba wanda ya samu kuri’u 931.
Tony wanda yake wakiltar mazabar Anambara ta Gabas da Yamma a majalisar dokoki ta kasa ya taba jagorancin kungiyar dalibai ta kasa wacce a takaice ake kira NANS.
Hakazalika ya yi takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben da aka yi a jihar tun shekarar 2013.
Sakamakon wannan nasara, a ranar 18 ga watan Nuwamban nan Nwoye zai kara da Gwamnan jihar Willie Obiano dan jam’iyyar APGA wanda yake neman sake yin takara karo na biyu tare da dan takarar jam’iyyar PDP da sauran ’yan takara daga wasu jam’iyyu.