✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nuna tsiraici: Fatima Ribadu ta nemi afuwa

Ta ce kamarar riga mai ruwan kasa da ta dora rigar fitar biki a kai ce ake ganin kamar ta nuna tsiraici

Diyar tsohon Shugaban Hukumar yaki da almundahada (EFCC) Nuhu Ribadu ta ba da hakuri game da kayan da ta sanya a ranar daurin aurenta wanda ya jawo ce-ce-ku-ce da zargin ta da nuna tsiraici.

Masu sharhi, musamman a shafukan zumunta sun yi ta sukar shigar da Fatima Ribadu ta yi bayan fitar hoton daurin auren nata na ranar Asabar inda take sanye da farar riga biki mai shara-shara daga samanta.

“Ina nadamar jin kunyar da kuskuren nawa ya ja wa abokai da dangina na kuma gode da yadda kuka yi tsaye wajen kare ni”, inji ta.

Fatima Ribadu ta bayyana takaici kan yadda aka yada hotunan nata da ta ce a cikin gida suka dauka amma suka karade shafukan zumunta.

Yayin bayar da hakuri, Fatima wadda ta auri Aliyu, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ta ce karamar rigar da ta dora doguwar rigar fitar bikinta a kai ce ta saje da fatarta shiya sa ake ganin ta bayyana tsiriacinta.

“Kamarar rigar mai ruwan kasa da na sanya ce aka yi tunanin cewa fatata ce – ba zan taba yin haka ba.

“Duk da haka na dauki laifin kunyatar da hakan ya jawo wa ’yan uwana da abokan arziki, na kuma dauki darasi”, inji sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram.