Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) Reshen Jihar Kogi ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani ma’aikacin Gidan Talabijin na Kasa (NTA), Chukwu Obiahu, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su bankado wadanda suka aikata laifin.
Rahotanni sun ce an kashe marigayi Chukwu ne ranar Talatar, bayan wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun yi masa ruwan duwatsu bayan ya taso daga wurin aiki da dare.
Shugaban kungiyar, Adeiza Momoh Jimoh, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a ranar Alhamis a Lokoja.
Yayin da yake ta’aziyya ga NTA kan rasuwar ma’aikacin, Momoh-Jimoh, ya nuna damuwa kan yanayin tsaro a kasar nan, inda ya ce matsalar na neman zama barazana ga harkokin mutane na yau da kullum.
“A kashe mutumin da ya je aiki don neman halal dinsa a kan hanyarsa ta komawa gida, ai wannan abun takaici ne matuka.
“A daidai wannan lokacin, ina kira ga ’yan sanda da su yi duk mai yiwuwa don gano wadanda suka aikata wannan laifi,” a cewarsa.