✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NNPP ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a Kano

NNPP ta ce ta dage zanga-zangar sai nan gaba

Jam’iyyar NNPP ta sanar dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi don nuna goyon baya ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Kano.

Tun da farko a cikin wata wasika da jam’iyyar ta aike wa Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, dauke da sa hannun Shugabanta na Jihar, Umar Haruna Doguwa, NNPP ta ce zanga-zangar ta goyon bayan INEC ce a kan wacce jam’iyyar APC ta yi.

NNPP ta shirya haduwa ne daga hekwatocinta na Kananan Hukumomi 44 sannan su wuce filin Dalar Gyada domin tafiya hekwatar ta INEC a ranar Alhamis.

To sai dai da Aminiya ta tuntubi Kakakin zababben Gwamnan na Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce sun dage ta daga ranar ta Alhamis zuwa wata ranar da za a sanar a nan gaba.

Aminiya ta rawaito yadda wasu kusoshin jam’iyyar APC mai mulkin Jihar, wacce ta fadi zaben Gwamnan Jihar suka gudanar da zanga-zanga a ofishin INEC na Jihar kan yadda hukumar ta ayyana dan takarar NNPP  a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sun kuma yi kira da a gaggauta cire Kwamishinan Zaben Jihar saboda abin da suka kira nuna fifiko ga jam’iyyar ta NNPP.

Rahotanni dai sun ce an samu tashin-tashina a yayin da APC ta yi zanga-zangar ta ranar Laraba, yayin da ’yan daba suka rika kai wa mutane hare-hare.