✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NNPP ta bukaci a soke zaben Gwamnan Borno

Jam’iyyar NNPP ta yi kira da a soke zaben Gwamnan Jihar Borno bisa cewa za a sunanta da tambarinta a takardun zaben jihar ba. Shugaban…

Jam’iyyar NNPP ta yi kira da a soke zaben Gwamnan Jihar Borno bisa cewa za a sunanta da tambarinta a takardun zaben jihar ba.

Shugaban Jam’iyyar, Barista Mohammed Mustapha ne ya sanar da hakan a zantawarsa da wakilinmu ta wayar tarho, wanda ya bukaci Hukumar INEC ta dakatar da hada sakamakon zaben, sannan ta gudanar da wani.

Jami’an tsaro sun kai samame wani gida kan zargin magudin zabe a Adamawa
“Za mu bi matakin da ya kamata domin kwato hakkinmu a kotu. Za mu bukaci kotu ta soke zaben sannan ta yi kira a sake zaben.
” Ba zai yiwu ba mu kashe kudadenmu wajen yakin neman zabe, sannan mu bata lokacinmu, sannan mu zuba ido INEC ta tafka irin wannan kuskuren.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin INEC hakan bai samu ba.