✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPCL zai mayar da ɗawainiyar matatun mai hannun ’yan kasuwa

NNPCL ya ɗauki matakin da zummar samar da man fetur din da zai wadatar da ƙasar.

Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya bayyana aniyarsa ta mayar da matatun man fetur na ƙasar da ke Warri da na Kaduna hannun ’yan kasuwa.

NNPCL ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Juma’a a shafinsa na X.

Kamfanin na NNPCL ya ce ya ɗauki matakin ne domin ci gaba da gudanarwa tare da kula da matatun biyu da zummar samar da man fetur din da zai wadatar da ƙasar.

An kafa matatar Warri — wadda ke Jihar Delta a yankin kudu maso kudancin ƙasar — a shekarar 1978.

Matatar na da ƙarfin da za ta iya tace gangar mai 125,000 a kowace rana, sannan tana iya tace wasu sinadaran masu alaƙa da albarkun man fetur.

An kafa matatar ne da nufin samar da mai ga yankunan kudanci da kudu maso yammcin ƙasar.

A ɗaya ɓangaren kuma, an ƙaddamar da matatar mai ta Kaduna — da ke Arewacin ƙasar — a shekarar 1980, domin samar da man fetur ga yankin Arewacin Nijeriya.

Matatar na da ƙarfin tace gangar 110,000 a kowace rana.