✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPCL ya musanta sayar da guraben aiki

Jama’a da dama na kwaɗayin aiki a NNPCL saboda albashi mai tsoka.

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta zargin da ake yi kan cewa yana sayar da guraben aiki.

NNPC ya ce duk wanda ya bari aka yaudare shi ya biya kuɗi domin samun aiki a kamfanin ya yi hakan ne bisa raɗin kansa.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in watsa labarai na kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Asabar.

Mista Soneye ya yi kira ga jama’ar Nijeriya musamman masu neman aiki da su yi watsi da wannan raɗe-raɗin.

Soneye ya kuma bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a labaran da ake yaɗawa kan cewa kamfanin yana da guraben aiki na sayarwa ga duk mai son saye.

Ya bayyana masu yaɗa irin waɗannan a matsayin ‘yan damfara waɗanda ke son su cuci masu neman aiki.

NNPC ya kuma yi gargaɗi kan cewa a matsayinsa na kamfani mai yin taka-tsan-tsan, ɗaukar aiki a kamfanin lamari ne da ake yin sa kai tsaye ba tare da buƙatar sayar da wani gurbi ba.

A farkon wannan wata na Agusta ne dai kamfanin na NNPCL ya sanar da cewa zai ɗauki aiki.

Sai dai kwana ɗaya da sanarwar, sai shafin da ake rajistar ɗaukar aikin ya samu matsala na wani ɗan lokaci sakamakon miliyoyin mutanen da suke ƙoƙarin shigar da bukatarsu ta neman aikin na NNPC.

Jama’a da dama na kwaɗayin aiki a kamfanin mai na NNPCL saboda albashi mai tsoka.