Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce kamfaninsu ya fi kowane takwaransa a duniya yin harkokinsa a fili babu kumbiya-kumbiya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci a kan kiranyen da Kwamitin Binciken Kudade na Majalisar Wakilai ya yi musu.
- Najeriya da Ghana: Najeriya ba za ta je gasar kofin duniya na 2022 ba
- ’Yan bindiga sun sake kashe mutane 23 a kauyukan Giwa
Kwamitin dai ya umarci dukkan Shugabannin sassan NNPC su bayyana a gabansa.
Mele Kyari, a cikin wata sanarwa ranar Talata ya ce kamfanin zai amsa gayyatar majalisar, sannan zai ci gaba da yin komai a fayyace.
“Babu abin da muke boyewa mai girma Shugaban kwamiti. Mun fahimci wannan kamfanin mallakin ’yan Najeriya sama da miliyan 200 ne, shi ya sa ma muka tsaya tsayin daka wajen kwatanta gaskiya, kuma haka za mu ci gaba da kasancewa.
“Babu kamfanin mai a duniya da ya kai mu yin abu a bayyane. Za mu bi umarnin kwamitin majalisar,” inji Kyari.
A ranar 16 ga watan Maris ce dai kwamitin, a cikin wata wasika da Shugabansa, Oluwole Oke, ya sanya wa hannu, ya yi sammacin sassan NNPC guda 17, a wani bangare na amsa binciken da Ofishin Babban Mai Bincike na Tarayya ke yi kan harkokinsu, tsakanin shekarun 2014 zuwa 2019.