✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nnamdi Kanu yana Ingila – Orji Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Mista Orji Uzor Kalu ya ce Shugaban kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biyafara ya sulale daga Najeriya zuwa Ingila ta…

Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Mista Orji Uzor Kalu ya ce Shugaban kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biyafara ya sulale daga Najeriya zuwa Ingila ta hanyar bi ta kasar Malesiya.

Nnamdi Kanu ya yi bace bat tun bayan da aka samu takaddama a tsakanin magoya bayansa da sojoji a kusa da gidansa da unguwar Afaraukwu da ke Umuahiya, fadar Jihar Abiya. 

Wannan fallasa ta Orji Kalu ta zo ne bayan lauyoyinsa Nnamdi Kanu sun garzaya Babban Kotun Abuja suna neman ta tilasta sojoji su fito da shi bisa zargin sojojin sun tafi da shi bayan sun kai farmaki a gidansa. Zargin da sojojin suka musanta.

Tsohon Gwamnan ya bayyana wa wata jarida a ranar Lahadin da ta gabata cewa, “Ba sojoji ne suka kama Kanu ba. Kanu ya tafi Malesiya ce daga can ya tafi Ingila. Nnamdi Kanu yana Landan a yanzun nan da muke Magana. Babu wanda ya kama shi. Ya bar kasar nan ne a kashin kansa.”

Tsohon Gwamna ya ce, wani dan uwan Kanu ne ya shaida masa inda jagoran masu neman a waren yake. Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor ya nuna mamaki kan yadda Kalu ya bayyana inda wanda yake karewa yake alhali ba ya nan a “ranar da sojoji suka kai farmaki gidan Kanu.”

Lauyan ya ce ya riga ya shigar da kara a kan batun yana bukatar a tilasta Babban Hafsan Sojin kasa, Laftana Janar Tukur Buratai ya gabatar da Kanu a gaban kotun.

Ejiofor da wadansu a cikin takardar karar sun yi da’awar cewa, Kanu wanda yake gidansa a lokacin da wasyu sojoji suka kai hari a ranar 14 ga Satumban bana, “ba a ganshi ko aka ji daga gare shi ba bayan kai masa mummunan hari da wakilan wanda ake kara (Hafsan Hafsoshin Sojan kasa) tun ranar 14 ga Satumban bana.”

A sanarwar da Ejiofor ya fitar ta Intanet ya ce: “Kalu yana neman yin amfani da halin da Kanu ya shiga ne domin neman tagimashi. Me kuke tsammani daga mutumin da yake da takaitaccen ’yanci, yake kokarin kwatar kansa daga zargin cin hanci? Yana neman tagomashi ne a inda babu ta hanyar kawar da hankali. Ga alama ya manta cewa ba shi ne Gwamnan Jihar Abiya ba.”

Ya ce kungiyar IPOB za ta bukaci Orji Kalu da Janar Buratai su bayyana a gaban kotu a ranar 17 ga Oktoban nan domin su shaida wa duniya abin da suka sani kan inda Nnamdi Kanu yake.