Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Kwamared Ayuba Wabba, ya yi Allah wadai da sabon kudurin da ake kokarin kirkirowa wanda zai haramta wa ma’aikatan lafiya shiga yajin aiki.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Talata, Wabba ya ce kudurin ya saba da tanade-tanaden dokokin kwadago na kasa da kasa da ma na cikin gida.
- Yadda ’yan banga suka hallaka ’yan bindiga 20 a Taraba
- 2022: Shugaban Karamar Hukuma ya gabatar da kasafin kudin N4.7bn a Kaduna
Ya ce, “Wannan abin dariya ne. Idan komai na tafiya yadda ya kamata babu wanda zai tafi yajin aiki.
“Saboda haka, wannan doka ce da ake kokarin kirkirowa da nake da tabbacin hatta masu kokarin yinta ba su san me ta kunsa ba.”
Kudurin dokar dai wanda ke neman a yi wa harkokin kwadago kwaskwarima, dan majalisar daga Jihar Enugu, Hon. Simon Chukwuemeka Atigwe ne ya gabatar a gaban zauren Majalisar Wakilai.
Shugaban ’yan kwadagon ya lura cewa damar shiga yajin aiki hakki ne na dukkan ma’aikaci wanda kuma ya hada da damar shiga kungiyoyi.
Ya ce, “Kundin yarjejeniyar kwadago mai shafi 751 ya yi bayani karara cewa ’yancin ’yan kwadago ne tafiya yajin aiki da shiga kungiyoyi, kuma ana amfani da su ne wajen kare muradu da kuma hakkokinsu.”