Kungiyoyin kwadago ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a a ranar Talata 8 ga Satumba, 2020, a Jihar Ribas.
Sun janye yajin aikin ne bayan taron tattauanwar da suka samu daidaito da Gwamantin Jihar kan takaddamar da ke tsakaninsu.
- Kungiyar IPOB ta kashe Hausawa a Jihar Ribas
- Sojoji sun fatattaki ‘yan ta’adda a Nasarawa da Binuwai
- Abin da ya da aka kara farashin mai —Buhari
A baya NLC na zargin Gwamnatin Jihar Ribas da daukar matakai da tsare-tsare masu takura wa ma’aikata da yakar kungiyoyin kwadago.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Ayuba Wabba ya ce bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar aiwatar da sabon mafi karancin albashi da sauye-sauyen a hakkokin ma’aikata masu alaka da karin.
Shugaban na NLC ya ce jihar za kuma ta bude sakatariyar kungiyar da a baya aka rufe saboda zargin wasu matsaloli.
Ya ce gwamnatin Jihar Ribas za ta ci gaba da biyan dukkanin hakkokin ma’aikata da kuma gudumunwarsu ga kungiyoyin kwadago.
Ayuba Wabba ya ce jihar ta amince ta biya albashin ma’aikatan lafiya da ta rike saboda yajin aikin da suka yi a 2017.
Bangarorin biyu sun kuma amince su kafa kwamiti mai bangarori uku domin daidaita biyan fansho da garatuti a jihar daidai da abin da Kudin Tsarin Mulki ya tanada.
Sun kuma yarda su janye dukkannin kararraki da suka shigar gaban kotu game da batutuwan da suke takaddama a kai.
Sannan babu ma’aikacin gwamantin jihar da za a uzzura wa saboda shiga yajin aiki ko sabanin da ke tsakanin ‘yan kwadago da gwamantin jihar.
Wabba ya yaba wa Gwamna Nyesom Wike bisa yadda ya nuna dattaku wajen magance matsalolin.
Gwamantin Ribas ta samu wakilcin Sakataren Gwamnatinta, Dakta Tammy Danagogo, da Shugaban Ma’aikata, Rufus Godwins, da Kwamishinan Yada Labarai, Paulinus Nsirim, da sauran wakilanta.
A daya bangaren, NLC ta samu wakilcin daga manyan jami’anta na da kuniyoyin ma’aikta ta TUC da na ‘yan fansho.